Fiye da shekara 100 ke nan ana kallon Hutu da Tutsi a yankin Manyan Tafkunan Afirka a matsayin ƙabilu biyu daban-daban, har ma a wasu lokuta ana bayyana su a matsayin jinsi daban.
Sai dai tarihi ya nuna cewa lamarin ya fi rikitarwa. Waɗannan sunaye sun wanzu tun kafin mulkin mallakar Turawa, amma ba su da tsayayyen ma’ana irin wadda suka samu daga baya.
Mulkin mallaka, musamman na Jamus da Belgium a Rwanda da Burundi, ya taimaka wajen sauya yadda ake kallon waɗannan ƙungiyoyi.
Turawan mulkin mallaka sun fara ɗaukar bambance-bambancen zamantakewa da siyasa a matsayin bambancin ƙabilanci mai tsauri.
Daga baya aka yi amfani da wannan rarrabuwar wajen fafutukar neman iko da mallakar ƙasa, da kuma batun wanda ya cancanci zama ɗan ƙasa.
Wannan tarihi ya taka muhimmiyar rawa a rikice-rikicen da suka biyo baya.
- Ronaldo ya ƙara matso kusa don cimma burin zura ƙwallaye 1,000
- FRSC ta ƙaddamar da yunƙurin kawo ƙarshen lodin wuce kima
- Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kama mutum biyu bisa zargin kisa
A Rwanda, tashin hankalin siyasa tsakanin Hutu da Tutsi ya ƙara tsananta a farkon shekarun 1990, musamman yayin yaƙin basasa tsakanin gwamnatin da Hutu ke jagoranta da ƙungiyar Rwandan Patriotic Front, wadda Tutsi suka fi yawa a cikinta.
A ranar 6 ga Afrilu 1994, an harbo jirgin shugaban Rwanda Juvenal Habyarimana da na Burundi Cyprien Ntaryamira, lamarin da ya haifar da ƙarin tashin hankali.
Bayan wannan hari ne aka fara kisan kiyashi a Rwanda.
A cikin kusan kwanaki 100, an kashe mutane tsakanin 800,000 zuwa miliyan ɗaya, galibinsu fararen hula Tutsi da kuma Hutu masu matsakaicin ra’ayi, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayin Hutu, jami’an gwamnati da mayakan sa-kai kamar Interahamwe na daga cikin waɗanda aka ɗora wa alhakin kisan.
Rikicin ya ƙare ne a watan Yulin 1994 bayan RPF ta kayar da gwamnatin tare da karɓe iko.
A Burundi ma, an shafe shekaru ana samun rikice-rikicen siyasa tsakanin Hutu da Tutsi.
A watan Oktoban 1993, an kashe shugaban ƙasar na farko da aka zaɓa ta hanyar dimokuraɗiyya, Melchior Ndadaye, wanda ɗan Hutu ne, yayin wani yunƙurin juyin mulkin sojoji.
Wannan ya jawo ƙarin kisan mutane da gudun hijira, sannan Burundi ta shiga yaƙin basasa wanda ya ɗauki fiye da shekaru goma.
Bayan kisan kiyashin Rwanda, rikicin ya bazu zuwa Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, musamman gabashin ƙasar.
Kimanin ‘yan Rwanda miliyan biyu ne suka tsere daga ƙasar bayan RPF ta karɓi iko a 1994, yayin da sama da miliyan ɗaya suka shiga yankin da a lokacin ake kira Zaire.
Wasu daga cikin waɗanda suka gudu sun haɗa da tsoffin sojojin Rwanda da mayakan Interahamwe, waɗanda daga baya wasu daga cikinsu suka sake shirya kai hare-hare kan gwamnatin Rwanda daga cikin Congo.
Masana daga yankin sun ce ba za a iya danganta rikice-rikicen gabashin Congo da Hutu da Tutsi kaɗai ba.
Batutuwan ƙasa, zama ɗan ƙasa, siyasa, iko kan yankuna da albarkatun ƙasa su ma suna taka muhimmiyar rawa.
Wannan abin da wasu masana ke kira gadon rarrabuwar kai na mulkin mallaka ne, wanda har yanzu ke tasiri kan siyasa, zama ɗan ƙasa da rikice-rikice a yankin Manyan Tafkunan Afirka.