Jagororin addini da masu sharhi kan batutuwan siyasa sun shawarci ‘yan takarar kujerun gwamnoni da na majaisun dokokin jahohi da su gudanar da yakin neman zaɓe cikin lumana da bin doka da oda.
Ustaz Sani Ibn Salihu da Dr Abdurrazak Inuwa da Adamu Ciroma na daga cikin waɗanda su kai kiraye-kirayen daidai lokacin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta Ta Ƙasa ta ba da umarnin fara gangamin yaƙin neman zaɓe ga masu takarar kujerun gwamnoni da ‘yan majalisun dokokin jihohi.
Ustaz Sani Ibni Salihu, wanda ya shawarci ‘yan siyasa da ka da su mayar da yakin neman zabe wani lamari na ko ai mutu, ko ai rai, ya tunatar da su cewa tuni fa Allah Ya zabi wanda Ya ke so.
Malamin har ila yau ya gargadi magoya baya da su nutsu, su kuma kaucewa barin ‘yan siyasa su yi amfani da su ta hanar da ba ta dace ba, don cimma bukatuynsu na siyasa.
-
Ronaldo ya ƙara matso kusa don cimma burin zura ƙwallaye 1,000
-
FRSC ta ƙaddamar da yunƙurin kawo ƙarshen lodin wuce kima
Shi ma Dr Abdurrazak Inuwa, wani dan jarida mai zamn kansa kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, tunawa ‘yan siyasar yai cewa kundin tsarin mulki ya fayyace yadda ‘yan takara ya kamata su gudanar da yakin neman zabe.
A nasa bangaren, Malam Adamu Ciroma, mai sharhi kan batutuwan siyasa shawartar ‘yan siyasar ya yi da su fi mayar da hankali ga gabatar wa da masu zabeirin shirye-shiryen dasuke da su, a maimakon yinamfani da cin zarafi ko tashin hankali.
Idan akai la’akari da irin dumin da siyasar kasar nan ke yi, irin wadannan kiraye-kiraye da shawarwari za su taimaka sosai wajen dawo da hankula ‘yan kasa kan abin da ya kamata yayin da ‘yan takara ke neman kuri’unsu.