Tobi Amusan ta jagoranci tawagar Najeriya zuwa lashe lambar Azurfa a ranar farko ta bude Gasar Ultimate Championships ta Duniya ta wasannin motsa jiki a Budapest, dake kasar Hungary, yayin da ta samu kyakkyawan sakamako a wasan karshe na tsere na mata na mita 100.
A halin yanzu, Amusan ta tsallake zuwa wasan karshe sakamakon ta zo ta biyu a wasan kusa da na karshe da minti 12 da dakika 49, inda ta biyo bayan ‘yar kasar Bahamas, Devynne Charlton wadda ta lashe gasar rukunin da minti 12 da dakika 45.
Shahararriyar ‘yar wasan Najeriyan ta inganta kokarinta a wasan karshe, inda ta gama a minti 12 da dakika 34 ta samu lambar azurfa, inda ‘yar Amurka, Masai Russell, ta lashe kambun da minti 12 da dakika 22. ‘
Yar kasar Netherlands, Nadine Visser, ta kammala matsayi na uku da minti 12 da dakika 39.
- Ronaldo ya ƙara matso kusa don cimma burin zura ƙwallaye 1,000
-
Lionel Messi ya cimma yarjejeniyar sayen kungiyar CD Eldense ta kasar Spaniya
- Yaya Touré ya kafa tarihi a gasar zakarun Turai
Lambar azurfar Amusan ta ba Tawagar Najeriya kyauta ta farko a gasar yayin da ‘yan wasan kasar suka fara kamfen dinsu da manyan ‘yan wasa na duniya.
Da farko, Ella Onojuvwevwo ta zo ta 6 a wasan kusa da na karshe na farkon wasan tsere na mata na mita 400 da minti 50 da dakika 50, inda ta kammala a matsayi na 12 gaba daya daga cikin ‘yan wasa 16 da suka fafata a gasar.
‘Yar Jamhuriyar Dominican, Marileidy Paulino, ce ta lashe wasan kusa da na karshe da minti 49 da dakika 58, yayin da ‘yar Bahrain Salwa Eid Naser ta zo ta biyu a minti na 49 da dakika 67.
Tawagar Najeriya za ta sake dawowa filin wasa a Rana ta 2, inda Ezekiel Nathaniel zai fafata a wasan kusa da na karshe na biyu na tsere na maza na mita 400, yayin da Kayinsola Ajayi zai shiga wasan kusa da na karshe na tsere na maza na mita 100 tare da manyan ‘yan wasan gudu na duniya.