Tambarin Hukumar FIFA

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya, FIFA, ta ce har yanzu ba ta yanke hukunci akan ƙasar da za ta ƙarfi baƙuncin wasan ƙarshe na Gasar Cin Kofin Duniya ta 2030 ba.

Wannan bayani ya ƙaryata ikirarin da ya gabata daga Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Marokko, Fouzi Lekjaa, na cewa za a buga wasan ƙarshe na Gasar Duniya a Marokko.

Kwanan nan Lekjaa ya bayyana cewa za a buga wasan ƙarshen a sabon filin wasa na Hassan II da ke Benslimane, kusa da Casablanca, inda ya gabatar da filin a matsayin zaɓin Marokko na karɓar baƙuncin babban wasan gasar.

FIFA ta jaddada cewa har yanzu ba a tantance filin wasan da za a buga wasan karshe ba kuma za a yanke shawarar a daidai lokacin da ya dace.

Wani mai magana da yawun FIFA ya shaida wa hukumar labarai ta Spaniya, EFE, cewa matsayin hukumar bai canza ba kuma “za a yanke shawara kan wurin wasan karshe a lokacin da ya dace.”

Wannan bayani ya zo ne a daidai lokacin da gasa ta karu tsakanin Marokko da Spaniya akan wadda za ta karbi bakuncin wasan karshe na Gasar Cin Kofin Duniya ta 2030.

FIFA ta kuma karyata rahotannin da suka fito a watan Agusta cewa Shugaba Gianni Infantino, ya yi wa Morocco alkawarin ba ta wasan karshe domin domin samun goyon bayana yayin zaben shugaban FIFA na shekara mai zuwa.

Hukumar kwallon kafa ta duniya ta ce wadancan rahotanni karya ne kuma suna bata wa mutane rai, inda ta dage cewa ba a cimma wata yarjejeniya ba kan wurin.

Ana sa ran sabon filin wasa na Marokko zai iya daukar masu kallo kusan 115,000, wanda zai iya sa ya zama daya daga cikin manyan filayen kwallon kafa na duniya. An tsara za a kammala ginin filin kafin gasar ta 2030.

A gafe guda, Spaniya ta nuna sha’awarta na karban bakuncin wasan karshen.

Filin wasa na Santiago Bernabéu a Madrid da na Camp Nou na Barcelona na daga cikin filayen da Spaniya ke la’akari da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *