Patrick Vieira ya bayyana aikin da aka bashi na horar da babbar tawagar kasar Senegal a matsayin “girmamawa abar alfahari” gabanin gabatar da shi a hukumance.
Ana sa ran za a gabatar da Viera a matsayin sabon kocin Senegal a ranar Juma’a, lokacin da zai bayyana jerin ‘yan wasansa na farko.
Viera mai shekaru 50, ya shahara a matsayin dan wasan kasar Faransa, inda ya buga wa kasar wasanni 107, amma an haife shi a birnin Dakar, dake Senegal a ranar 23 ga watan Yunin shekarar 1976.
Vieira ya zauna a Senegal har sai da ya kai shekara takwas lokacin da ya koma Faransa tare da iyayensa, inda ya fara sana’ar kwallon kafa a can tare da ƙungiyar Cannes.
-
An shiga rana ta ƙarshe a taron Hukumar FIFA da CAF a Najeriya
-
NPFL: Sporting Lagos ta yi nasara a waje, Barau ta lallasa Ranchers Bees
-
Najeriya ta yi wa New Caledonia wankan tsarki da ci 10-1
Bai koma Senegal ba sai a 2003, lokacin da ya zama babban tauraro a Arsenal da Faransa, inda ya daura turbar ginin sabuwar makarantar koyon ƙwallon kafa a kasar.
Tsohon kyaftin din na Gunners ya sake komawa Senegal, a wannan karon a matsayin kocin tawagar ƙasar, inda ya maye gurbin Pape Thiaw.

Vieira ya rubuta a shafin sa na Instagram cewar “Abun girmamawa ne da alfahari na shiga Senegal a matsayin babban kocin tawagar ƙasar.”
“Ina godiya ga Hukumar Kwallon Kafa ta Senegal saboda kwarin gwiwar da ta nuna a kaina- Ina jiran haduwa da tawagar da kuma fara aiki tare a mataki na gaba,” in ji Vieira.
Senegal, ta sha takaicin shan kashi a gasar cin Kofin Duniya da aka kammala, bayan da ta tsallake rijiya da baya daga rukuninta, inda ta doke Iraki da ci 5-0 bayan ta sha kashi a hannun Faransa da Norway.
Bayan kammala gasar ne hukumomi a kasar ta Senegal suka sallama Pape Thiaw, kafin daga bisani a mika ragamar tawagar hannun tsohon Kyaftin din Arsenal Patrick Vieira.
Vieira zai fara gwada horar da tawagar kasa da kasa a karon farko bayan ya horar da kungiyoyin kwallon kafar New York City FC, da Nice, da Crystal Palace, da Strasbourg da kuma Genoa.
Ya bar Genoa a watan Nuwambar 2025 bayan ya jagoranci wasanni 37, inda ya samu nasara 10.
Wasannin farko da sabon kocin zai jagoranta za su kasance na neman gurbin shiga gasar cin Kofin Afirka (AFCON) da Mozambique da Habasha daga baya a wannan watan.
