Farashin man fetur na ci gaba da sauyawa a Najeriya, lamarin da ke ƙara jawo damuwa ga ’yan ƙasa, musamman masu amfani da motoci da masu sana’o’in da suka dogara da sufuri.

To, me ke jawo ci gaba da hauhawar farashin sa? kuma me ya sa ’yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar wannan matsala duk da kasancewar ƙasar na daga cikin masu arzikin ɗanyen mai?

Masani harkar man fetur da dangogin sa, Kwamared Alhassan Uba Idris, ya ce matsalolin da suka shafi matatun man Najeriya na daga cikin abubuwan da ke shafar samar da man fetur din a cikin gida.

A wata tattaunawa da Gidan Reddiyon Blueprint a Abuja, Alasan Uba ya bayyana cewa a ganinsa, matatun man Najeriya ba sa ne aiki yadda ya kamata, lamarin da ya sanya ƙasar ke ci gaba da fuskantar mummunan gibin samun isasshen tataccen man fetur da zai wadace ta a cikin gida.

Masanin ya kara da cewa, hauhawar farashin man ya na da tasiri kai tsaye kan harkokin sufuri da kayan masarufi, wannan ta sanya kuɗaɗen sufuri da jigilar kaya da farashin kayan masarufi ke hauhawa.

“Najeriya na da ɗimbin ɗanyen mai, amma samun albarkatun mai kaɗai ba ya tabbatar da samun isasshen tataccen man fetur a farashi mai sauƙi. Akwai buƙatar samar da ingantaccen tsarin tace ɗanyen mai a cikin gida da kuma tabbatar da wadatar kayayyakin man fetur,” Inji shi.

Kasancewar matatar Dangote da sauran matatun cikin gida na ƙara jawo tambayoyi kan yadda za’a rage dogaro da shigo da tataccen man fetur daga ƙasashen waje, al’amarin siyasar mai a Najeriya abune da aka gaza shawo matsalolin dake dabaibaye dashi kawo yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *