Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC, ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakan gaggawa domin rage wa ’yan Najeriya radaɗin tashin farashin man fetur.
Kungiyar ta ce a yanzu ana sayar da litar man fetur da kusan naira dubu ɗaya da ɗari huɗu da talatin a wasu gidan man fetur, yayin da farashin ke ƙara hauhawa a wasu wuraren da ke da wahalar kai man.
Shugaban kungiyar, Joe Ajaero, ya ce tashin farashin man fetur zai ƙara tsadar sufuri da abinci da ƙuɗin haya da na makarantu da sauran muhimman buƙatun yau da kullum.
Kungiyar kwadagon ta buƙaci gwamnati ta samar da tallafin albashi mai ma’ana ga ma’aikata domin rage musu matsin tattalin arzikin da suke fuskanta.
Haka kuma kungiyar ta buƙaci gwamnati ta tabbatar da cewa ana sayar da ɗanyen mai ga matatun man da ke cikin Najeriya da kuɗin naira, domin taimakawa wajen samar da man fetur a cikin gida da kuma rage dogaro da sauye-sauyen farashin kasuwar duniya.
NLC ta kuma nemi a ƙara karfin ajiyar man fetur na ƙasa, tana mai cewa hakan zai taimaka wajen tabbatar da tsaron makamashi da kuma tunkarar irin wadannan matsaloli a lokutan gaggawa.
Kungiyar ta ce bai kamata a kawar da yiwuwar tallafin gwamnati ba a irin wannan yanayi.
Joe Ajaero ya ce ƙasashen da ke samar da man fetur na ɗaukar matakai daban-daban domin kare al’ummarsu daga tasirin matsalar makamashi ta duniya, don haka Najeriya ma ya kamata ta ɗauki matakan rage wa jama’a radaɗi.