Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Abuja ta yanke wa wata baiwar Allah ’yar kasuwa hukuncin zaman kaso na shekara 27 bayan ta same ta da laifin safarar miyagun kwawoyi.

Mai shari’a Hauwa Joseph Yilwa, wacce ta yanke hukuncin, ta yanke wa matar hukuncin ne a kan tuhuma biyu biyun da ake yi mata: daurin shekara 12 a kan tuhuma ta farko, shekara 15 kuma a kan tuhuma ta biyu.

Hukumar Yaki da Ta;ammali da Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ce ta shigar da kara a kan ’yar kasuwar, wacce uwa ce ga ’ya’ya uku.

Sai dai, ganin yadda wacce aka yanke wa hukuncin ta nuna nadama a duk tsawon lokacin shari’ar, kuma bisa la’akari da cewa wannan ne laifinta na farko, uwa uba kuma ba ta bata wa kotu lokaci ba wajen amsa laifinta, Mai Shari’ar ta ba da umarnin cewa hukunce-hukuncen su yi aiki a lokaci guda.

Da wannan umarni, matar za ta shafe shekaru 15 ne kawai a gidan yari.

Mai Shari’a Yilwa ta kuma ce ko da yake mai laifin ta nuna nadama, ta’ammali da miyagun kwayoyi abu ne da bai kamata a dauke shi da wasa ba saboda illar da yake da shi ga kasa da ma duniya baki daya.

Ta nuna matukar bacin ranta ganin cewa an kama matar da miyagun kwayoyi masu nauyin kilo 250.

Lauyan wacce aka tuhuma, Barista D. I. Badams, ya yi magiya ga kotun da ta yi sassauci wajen yanke hukuncin, bisa la’akari da alkawarin da wacce aka yanke wa hukuncin ta yi cewa ba za ta sake komawa ta’ammali da miyagun kwayoyi ba a rayuwarta.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *