Tawagar Falconets ta Najeriya za ta fafata da Colombia a wasan kwata-fainal na Gasar Cin Kofin Duniya ta mata ‘yan ƙasa da shekaru 20 ta 2026 da ake bugawa a Poland, bayan da ‘yan Kudancin Amurkan suka doke mai masaukin baƙi Poland da ci 1-0 a ranar Alhamis.

Za a buga wasan kwata-fainal din ne a ranar Lahadi, 20 ga Satumba, da misalin karfe 6:30 na yamma agogon Najeriya a filin wasa na Stadion Miejski ŁKS Łódź da ke Łódź.

Colombia ta tabbatar da samun gurbi a wasan kwata-fainal bayan ta doke mai masaukin baki Poland a wasan zagaye na 16, inda za ta yi zzafan haduwa da Falconets.

Tawagar Falconets ta Najeriya ta tsallaka zuwa wasan kwata-fainal ne bayan doke Ingila da ci 3-0.

Tosin Rafiu ce ta fara ci wa Najeriya ƙwallo a minti na 8, kafin Seimeyeha Janet Akekoromowei ta ƙara ta biyu, bayan minti biyu da dawowa daga hutun rabin lokaci.

Sannan Mary Mamudu ta cikata ƙwallaye na uku a minti na 73 inda hakan ya tabbatarwa Falconets da gagarumar nasara akan Ingila.

Bayan ta cire Ingila cikin salo mai kayatarwa, Najeriya za ta shiga wasan kwata-fainal da kwarin gwiwa da kuma fatan kaiwa wasan kusa da na karshe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *