Rundunar sojin Uganda ta ce ta dakatar da duk wani haɗin gwiwar tsaro da na soji da Turkiyya, bayan matsin lamba da Kampala ke yi wa Ankara domin ta mika mata wani fitaccen ɗan siyasa mai sukar Shugaba Yoweri Museveni.
Shugaban rundunar sojin Uganda, Muhoozi Kainerugaba, wanda ɗan Museveni ne kuma ake ganin zai iya maye gurbinsa a nan gaba, ya sha samun saɓani da hukumomin Turkiyya kan ƙoƙarin tasa keyar Fred Lumbuye zuwa Uganda.
- An kashe mutum biyu a harin da Ukraine ta kai Moscow – Rasha
- Babu yiwuwar AI ta jawo ƙarshen duniya a 2030-Jensen Huang
- Ɗalibin tukin jirgi da mai koyar da shi sun mutu a hadarin jirgi a Kenya
Lumbuye na fuskantar tuhume-tuhume 15 da suka haɗa da tunzura jama’a, da kuma yaɗa bayanan ƙarya.
A ranar Juma’a, dubban ’yan Uganda da ke cikin ƙungiyar Patriotic League of Uganda, wata ƙungiyar farar hula da siyasa da ke da alaƙa da Kainerugaba, sun gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Turkiyya da ke Kampala, babban birnin ƙasar.
Kakakin rundunar sojin Uganda, Chris Magezi, ya ce a cikin wata sanarwa cewa Rundunar Tsaron Jama’ar Uganda (UPDF) ta dakatar da duk wani haɗin gwiwar tsaro da na soji da Jamhuriyar Turkiyya.