Najeriya ta samu nasarar gudanar da aikin tiyata na farko ta hanyar mutum-mutumi daga nesa, wanda aka fi sani da tele-robotic surgery.

An gudanar da aikin ne ta haɗin gwiwar Redeemer’s Health Village (RHV), RoboMed Global da Nisa Premier Hospital.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an gudanar da aikin tiyatar ne kai tsaye ranar Asabar, daga na’urar Toumai console da ke RHV, a kan wani mara lafiya da ke Nisa Premier Hospital a Abuja.

An dai cirewa maralafiyar ƙodar dama da ke ɗauke da ƙwayar cutar daji, ta hanyar amfani da fasahar mutum-mutumi da sadarwa daga nesa.

Tele-robotic surgery, wato tiyatar daga nesa, wata fasaha ce da ke bai wa likita damar gudanar da aikin tiyata a kan mara lafiya da ke wani wuri daban da inda likitan yake.

Farfesa Obi Ekwenna-Davis, kwararre a fannin cututtuka da tiyatar hanyoyin fitsari da gabobi ne ya jagoranci aikin, ya ce wannan nasara ta nuna cewa za a iya gudanar da tiyata ta hanyar sadarwa daga nesa cikin aminci ga marasa lafiya da ke sassa daban-daban na Najeriya da ma duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *