Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT, Nyesom Wike, ya ce za a kammala manyan ayyukan raya ababen more rayuwa da ake gudanarwa a Abuja tare da miƙa su ga jama’a zuwa watan Janairu na shekarar 2027.
Wike ya bayyana hakan ne bayan ya zagaya domin duba yadda ayyukan manyan tituna da gadoji ke gudana a wasu sassan Abuja, ciki har da aikin titin Inner Southern Expressway, ISEX, Southern Parkway da kuma hanyar da ta taso daga yankin Jami’ar Nile zuwa Ring Road 3.
- NAF ta fara sayen jirage masu saukar ungulu 12 kirar AH-1Z Viper
- Zuwan Blueprint Radio cigaba ne ga Najeriya–Ministan Watsa Labarai
Ministan ya ce kamfanin CGC Nigeria Limited, wanda ke aikin ISEX, ya tabbatar masa cewa zai kammala aikin tare da miƙa shi a watan Disamba na shekarar 2026. Ya kuma ce kamfanin CCECC da ke aikin hanyar Jami’ar Nile zuwa Ring Road 3 ya yi alkawarin kammala aikin a makon farko na Janairu 2027.
Da yake magana kan aikin Southern Parkway da ake gudanarwa a Gaduwa, Wike ya ce an samu jinkiri wajen fara wasu ayyukan shimfiɗa ƙasa saboda yawan ruwan sama. Sai dai ya ce za a ci gaba da aikin da zarar damina ta ragu, domin a kammala aikin kafin zaɓen da ke tafe.
Wike ya ce ya gamsu da yadda ayyukan ke gudana, yana mai cewa ’yan kwangilar sun sake tabbatar masa da cewa za su cika alkawuran da suka dauka na kammala ayyukan cikin lokacin da aka tsara.
Ministan ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na son ganin an kammala ayyukan da aka fara a Abuja domin jama’ar babban birnin tarayya su amfana da su.