Bankin Duniya ya amince da bai wa Najeriya sabon rancen dala biliyan 1.25 a ƙarƙashin shirin gwamnatin Najeriya na bunƙasa zuba jari da ƙara samar da ayyukan yi (NAIJA), duk da ci gaba da damuwar jama’a kan yadda bashin ƙasar ke ƙaruwa da kuma kiraye-kirayen da ake yi wa gwamnatin tarayya ta rage yawan karɓar bashin ƙasashen waje.

Bankin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar tare da ƙaddamar da sabon tsarin haɗin gwiwa da Najeriya na shekarun 2026 zuwa 2032.

A cewar bankin, sabon tsarin zai mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi ta hanyar bunƙasa saka hannun jari daga kamfanoni masu zaman kansu da kuma ƙarfafa ci gaban tattalin arziki.

Bankin ya ce wannan sabon rancen zai taimaka wajen aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da suka haɗa da bunƙasa kasuwannin hannayen jari, da inganta dokokin tattalin arzikin zamani da na gwamnati ta yanar gizo, da faɗaɗa samar da wutar lantarki, da rage shingayen kasuwanci tsakanin ƙasashen ECOWAS da yankin ciniki na AfCFTA, da inganta iri na noma da kuma ƙara yawan kuɗaɗen shiga na gwamnati.

Haka kuma, sabon tsarin haɗin gwiwar na da burin samar da wutar lantarki ga mutum miliyan 32,  da haɗa mutum miliyan 58 da intanet, da inganta harkokin lafiya da abinci mai gina jiki ga mutum miliyan 40, tare da tallafa wa manoma miliyan 9.5 domin ƙara yawan amfanin gona da bunƙasa jarin ɗan Adam.

Daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Verghis, ya ce manufar ita ce a tabbatar sauye-sauyen tattalin arzikin da aka samu sun haifar da ingantuwar rayuwar al’umma ta hanyar samar da ayyukan yi da jawo ƙarin masu zuba jari.

 

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *