Tsohon Gwamnan Jihar Edo kuma Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya bayyana goyon bayansa ga shirin Gwamnatin Jihar Edo na harbe mutanen da aka kama da laifin yin garkuwa da mutane da bindiga.
Oshiomhole ya bayyana haka ne yayin da yake magana da magoya bayansa a bikin kaddamar da kamfen din zaben kananan hukumomi na jam’iyyar APC a garin Auchi, Jihar Edo.
A cewar sa, matakin zai kawo karshen aikata manyan laifuka, kuma jihohi na da ikon yanke hukuncin da ya dace kan laifukan da ake aikatawa karkashin ikon su.
-
Yaran Borno da aka sace: ‘Ba mu san ko yaranmu suna raye ba’- Iyaye
-
Dillalan Man Fetur sun yi barazanar rufe gidajen mai idan…
“Gwamnan Jihar Edo, Okpebholo ya bayyana cewa muna cikin tsarin tarayya. Kamar yadda yake ake gani a Amurka, kowace jiha na da hakkin kafa dokoki kan hukunci idan ya zo ga laifukan da ake aikatawa a cikin su.
Hukuncin laifin satar mutane da kisan kai na karkashin ikon jihohi ne, illa iyaka tuntubar zauren Majalisar Dokokin ya ragewa bukatar sauya hukuncin rataya zuwa harbi da bakin bindiga,” in ji Oshiomhole.
Ya ce hukuncin da aka shirya zai zama darasi ga wadanda ke tunanin yin garkuwa da mutane su sauya tunaninsu.
“Wadanda ba su son hakan ya faru da su, kada su zo Jihar Edo. Don haka, muna tsayawa muna ba shi cikakken goyon baya,” in ji shi.
Oshiomhole ya kuma maimaita goyon bayansa ga kafa ‘yan sandan jiha, yana cewa hakan zai karfafa yaki da rashin tsaro.
“A matsayina na Sanatanku, na goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da shawarar da Taron Gwamnonin suka yanke na kafa ‘yan sandan jiha,” in ji shi.
