Bassirou Faye Shugaban Senegal

Shugaban ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, na shirin ƙaddamar da sabuwar jam’iyyar siyasa, lamarin da ke nuna ƙarshen alaƙarsa da tsohon Firaminista, Ousmane Sonko, yayin da rikicin siyasar shugabannin ƙasar ke ƙara tsananta gabanin zaɓukan ƙananan hukumomi da kuma sauye-sauyen kundin tsarin mulki.

Ƙungiyar da ke mara wa Shugaba Faye baya ta bayyana cewa ya fara shirye-shiryen kafa sabuwar jam’iyyar siyasa

A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a daren Juma’a, ta ce Faye ya bai wa babbar mai ba shi shawara, Aminata Touré, jagorancin wata kwamitin aiki da zai tsara da kuma kafa sabuwar ƙungiyar siyasar.

Wannan mataki shi ne mafi ƙarfi da ke nuna cewa dangantakar siyasa tsakanin Faye da tsohon abokinsa Ousmane Sonko ta ruguje.

Tun bayan hawansa mulki, Faye ya ci gaba da kasancewa mamba a jam’iyyar Pastef, amma dangantakarsa da Sonko ta fara tsami a cikin watannin baya kafin daga bisani shugaban ƙasar ya cire shi daga muƙamin Firaminista a watan Mayu.

Ƙaruwar wannan rikicin siyasa na zuwa ne a daidai lokacin da Senegal ke fama da matsin tattalin arziki, bayan da aka gano cewa gwamnatin da ta gabata ta bayar da bayanan da ba su dace ba game da yawan bashin da ƙasar ke bi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *