Gwamnatin Tarayya ta ce ta n

a ƙara ƙaimi wajen tabbatar da yi wa dukkan ‘yan Najeriya rajistar shaidar zama ɗan ƙasa ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Ƙasa da Hukumar NIMC.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin da ya karɓi Darakta Janar ta Hukumar NIMC, Dakta Abisoye Coker-Odusote, da tawagarta.
- CBN ya ce tsohuwar da sabuwar takardar kuɗin Naira 100 duk suna nan a matsayin halastattun kuɗaɗen mu’amala
- Majalisar Wakilai ta yi fatali da buƙatar gayyato Tinubu
Ya ce ingantaccen tsarin tantance ‘yan ƙasa yana da matuƙar muhimmanci wajen tsara manufofin gwamnati, da bunƙasa tattalin arziki, da sauƙaƙa ayyukan gwamnati ta hanyar fasahar zamani da kuma aiwatar da manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Ministan ya ƙara da cewa an riga an yi wa sama da mutum miliyan 136 rajista, amma har yanzu akwai kusan mutum miliyan 100 da ke buƙatar shiga cikin tsarin.