Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa takardar kuɗin Naira 100 ta yau da kullumBabban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa takardar kuɗin Naira 100 ta yau da kullum na ci gaba da kasancewa halastacciyar kuɗin mu’amala a faɗin ƙasar.
Yana mai jaddada cewa dole ne a karɓe ta wajen gudanar da harkokin kasuwanci da sauran mu’amaloli.
- Majalisar Dattawan ta nesanta kanta dangane da hukumar da ake taƙaddama a kanta
- Haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba: An kama sama da mutum 200 a Afirka ta Kudu
A wata sanarwa da Daraktar Riƙo ta Sashen Hulɗa da Jama’a na bankin, Hakama Sidi-Ali, ta fitar ranar Laraba, CBN ta ce hankalinta ya karkata kan rahotannin da ke nuna cewa wasu mutane da ‘yan kasuwa suna ƙin karɓar takardar kuɗin Naira 100 ta yau da kullum saboda kuskuren fahimtar cewa ba ta da inganci.
Bankin ya nanata cewa duka takardar Naira 100 ta yau da kullum da kuma ta musamman da aka fitar domin bikin cika shekaru 100 da haihuwar Najeriya, suna nan a matsayin halastattun kuɗaɗen da doka ta amince da su.