Gwamnatin Tarayya ta farfaɗo da wasu ayyukan dakunan karatu na intanet (e-libraries) guda 16 da aka watsar a Kwalejojin Tarayya (Federal Unity Colleges), a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin zamantar da makarantun gwamnati da kuma bunƙasa ilimi mai dogaro da fasaha.

Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, shi ne ya bayyana hakan yayin da yake ƙaddamar da sabon dakin karatun na intanet da cibiyar kiraye-kiraye na fasaha da aka inganta a Kwalejin Gwamnatin Tarayya (FGC) da ke Kano.

Bisa bayanin da aka samu daga sanarwar ma’aikatar, cibiyar tana sanye da tsarin wutar lantarki ta hanyar rana (solar power) da na’urorin sanyaya muhalli (air conditioning) da  fitilun zamani da kuma teburan kwamfuta kusan 80 domin tallafawa harkar koyarwa, koyo, da bincike.

Alausa ya bayyana cewa wannan aiki yana nuna jajircewar gwamnatin shugaba Tinubu wajen faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimin fasahar zamani.

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin ta gado ayyukan dakunan karatu na intanet guda 36 da aka watsar a duk faɗin Kwalejojin Tarayya, amma ta kammala guda 16 ta hanyar sa-stutun Hukumar Haɓaka Ilimin Fari ta Kasa (UBEC).

Ya ƙara da cewa abubuwan inganta fasaha na zamani za su ci gaba da kasancewa muhimmin sashe na ajandar yi wa fannin ilimi gyara ta gwamnati, sannan ya yi alkawarin ci gaba da zuba jari a ilimi mai matuƙar dogaro da fasaha.

A yayin ziyarar, Alausa ya kuma duba Makarantar Harshe Biyu (Bilingual School) da ke Ungogo, wanda ya ce aikinta ya kai kusan kashi 90 cikin 100 na kammaluwa, sannan ya ba jami’ai umarnin fara ɗaukar malamai aiki kafin buɗe makarantar da aka tsara yi a watan Satumba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *