Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa mai zaman kanta ta Najeriya (ICPC) ta gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, da tsohon Babban Mashawarcinsa, Jimi Adebisi Lawal, da wasu mutum biyar a gaban kotu bisa zarge-zargen cin hanci da halasta kuɗaɗen haram da sauran laifuka masu alaƙa da kwangilar CCTV da kuɗinta yakai naira biliyan 8.68.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na ICPC, John Money, ya fitar ranar Alhamis a Abuja, ya ce an shigar da sabuwar takardar tuhuma mai ƙunshe da tuhume-tuhume guda 11 a gaban Mai Shari’a Hauwa’u Buhari ta Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna, mai lamba FHC/KD/93C/2026.
Sanarwar ta bayyana cewa waanda ake tuhuma sun haɗa da Malam Nasir Ahmad El-Rufai da Mista Jimi Adebisi Lawal da kamfanonin Singularity Network Security Limited da Solar Life Nigeria Limited da Knowledge Investment Nigeria Limited da Intercellular Nigeria Limited da Noble Coast Resources Limited.
- Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabon titin mahaɗar hanyar Jahi zuwa Gwarimpa a Abuja
- Ƙudirin kafa ’yan sandan jihohi na ƙara samun goyon baya a Nijeriya
- Dakarun Operation Hadin Kai sun ceto mutane 53 a Biu
Hukumar ta kuma bayyana cewa Bashir El-Rufai, wanda aka ce ɗan uwan tsohon gwamnan ne kuma yana gudun hijira, an ambace shi a cikin ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen.
ICPC ta zargi El-Rufai da cewa yayin da yake gwamnan Jihar Kaduna a shekarar 2015, ya amince da bayar da kwangilar bincike, tsara aiki, zane na ƙarshe da girka na’urorin sa ido na CCTV a cikin birnin Kaduna kan kuɗin da aka sake dubawa na Naira 8,682,574,054.94 ga kamfanin Singularity Network Security Limited, duk da cewa kamfanin ba shi da ƙwarewar da ake bukata, kuma hakan ya saba da dokokin sayen kayayyaki da ayyukan gwamnati.
Hukumar ta kuma yi zargin cewa kuɗaɗen da aka samu daga wannan kwangila an rika tura su ta hannun wasu kamfanoni da mutane daban-daban, inda ake zargin cewa kuɗaɗen sun kasance haramtattun kuɗaɗe bisa tanadin dokar Hana da yaki da halasta kudaden haram ta shekarar 2022.
Bayan an karanta musu tuhume-tuhumen a kotu, El-Rufai da Jimi Lawal sun musanta dukkan zarge-zargen da ake yi musu.
Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 1 ga Yuli, 2026, domin yanke hukunci kan buƙatar bayar da belin waɗanɗa ake tuhuma.