Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU), tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Portugal, sun ba da gudunmawar ƙananan jiragen ruwan sintiri guda biyu masu tsawon mita 8.9 (rigid-hull inflatable patrol boats) da kuma kayan binciken laifuka na kimiyya (forensic equipment) ga Hukumar Sojin Ruwa ta Najeriya. 
Wannan tallafi an yi shi ne don ƙarfafa yaki da fashin teku da kamun kifi ba bisa ka’ida ba da fataucin miyagun kwayoyi, da sauran laifukan teku a yankin Tekun Guinea. 
An miƙa kayayyakin ne a ranar Talata a Cibiyar Horar da Tsaron Teku ta Gudunmawa (JMSTC) da ke Navy Town, Ojo, a Jihar Legas. Wannan shiri yana ƙarƙashin aikin “Taimako ga Tsaron Teku na Ƙasashen Yammacin Afirka” (SWAIMS), wanda shiri ne da EU ke ɗaukar nauyinsa, kuma ƙasar Portugal ke aiwatar da shi don inganta tsaron teku a duk faɗin ƙasashen ƙungiyar ECOWAS. 
Yayin da yake wakiltar Shugaban Ma’aikatan Sojin Ruwa (CNS) Mataimakin Admiral Idi Abbas, Babban Jami’in da ke Jagorantar Rundunar Sojin Ruwa ta Yamma, Rear Admiral Abdullahi Abubakar Mustapha, ya bayyana cewa waɗannan kayayyaki da aka bayar za su inganta sanya idanu, ɗaukar mataki cikin gaggawa, da kuma ƙarfin gudanar da doka na Hukumar Sojin Ruwa.
Ya tunatar da cewa an cire Najeriya daga jerin ƙasashen da fashin teku ya yi wa katutu na Hukumar Kula da Teku ta Duniya (IMB) a shekarar 2021.
Wannan nasara ta faru ne sakamakon ɗorewar sintiri da sanya idanu, da kuma ayyukan tabbatar da doka da Hukumar Sojin Ruwa ta gudanar a teku.
Ya ƙara da cewa sabbin jiragen ruwa da kayan binciken na forensic da aka bayar za su zama babban taimako wajen ɗorewa da kuma haɓaka nasarorin da ƙasar ta samu a fannin tsaron teku. 
Jakadan EU a Najeriya, Gautier Mignot, ya bayyana wannan kyauta a matsayin wani ɓangare na dogon buri da sadaukarwar Kungiyar Tarayyar Turai wajen ƙarfafa tsaron teku a Yammacin Afirka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *