Mataimakin Shugaban ƙasar Najeriya Kashim Shettima, ya shiga rukunin shugabannin duniya a taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.
Shettima, wanda ke wakiltar Shugaba ƙasa Bola Ahmed Tinubu, zai gabatar da jawabin Najeriya a gaban babban taron a yau Alhamis, 24 ga Satumba.
Ana sa ran zai bayyana matsayin gwamnatin Najeriya kan wasu manyan batutuwan duniya, da suka haɗa da zaman lafiya da tsaro, sauyin yanayi da ci gaba mai ɗorewa da kuma sake fasalin hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya.
Taron bana na Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda zai ci gaba har zuwa 28 ga Satumba, na gudana ne karkashin taken “Maido da amana, tafiyar da sauye-sauyen da ke samar da sakamako ga kowa.”
Shettima ya halarci wani taron karin kumallo da Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, ya shirya domin shugabannin tawagogin ƙasashe da iyalansu.
A yayin taron, ya kuma wakilci Shugaba ƙasa Bola Tinubu a taron Africa Minerals Strategy Group, inda ya yi kira ga ƙasashen Afirika da su daina dogaro da fitar da ma’adinai ɗanye, su maida hankali wajen sarrafa albarkatun cikin gida domin samar da ayyukan yi da bunƙasa masana’antu.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma ce haɗin gwiwar ƙasashen Afirika na da muhimmanci wajen tabbatartabbatar da cewa arzikin ma’adinai na nahiyar ya zama sanadin bunƙasar tattalin arziki da inganta rayuwar al’ummarta.