Shehin Malamin yayi zargin goyon bayan da yake baiwa Falasdinawa ne ke jawo masa bakin jini

Shahararren malamin addinin Islamarnan Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya zargi wasu kafafen yada labarai da sauya sanarwar da ya fitar a ranar 23 ga watan Mayu.

Yayin wani taron manema labarai da ya kira yau a gidan sa dake Kaduna, Malamin yace an sauyawa kalaman sa ma’ana dai dai da wani sako da ya taba wallafawa a shafinsa na Facebook, a watan Nuwamban shekarar 2025.

Sheikh Gumi yace wani likita dake zaune a Amurka ne ya turo masa wani sako ta WhatsApp, yana zargin cewa wasu kungiyoyi na shirin shirya gawarwakin bogi, domin ruruta jita-jitar cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.

Gumi ya bayyana cewa, lokacin da ya raba wannan sako ga mabiyansa, ya karkare ne da kalmar gargadi inda yake fadin “Ina fata hakan ba gaskiya ba ne!” Amma abin mamaki, sai wasu kafafen yada labarai suka riki labarin kamar shi ne da kansa yake yin wannan zargi.

Da yake jawabi dangane da tsohuwar takaddamar nan ta Umar Faruk Abdulmutallab dake tsare a Amurka kuwa, Sheikh Gumi ya sake fayyace cewa bashi da wata alaka ta ta’addanci da matashin.

Ya bayyana cewa a shekarar 2009, mahaifin Abdulmutallab ya neme shi domin ya tattaunawa da dansa tare da yi masa wa’azi bayan da matashin ya yanke hulda da mahaifa da yan uwansa.

Kodayake wata takardar sirri da shafin *WikiLeaks* ya wallafa a shekarar 2011, ta ambaci sunansa cikin wadanda ake zargi, Sheikh Gumi ya jaddada cewa hukumomin kasar Saudiyya sun gudanar da bincike mai zurfi a kansa, tare da wanke shi.

Yace wannan wankewa ce ma ta ba shi damar kammala karatunsa na digirin-digirgir (PhD) a kasar, kuma ya ci gaba da zirga-zirga zuwa Saudiyya ba tare da wata matsala ba.

Malamin ya bayyana cewa yana kyautata zaton matsayar da ya dauka na goyon bayan al’ummar Falasdinawa, da karbar bakuncin Jakadan Falasdinu a gidansa dake Kaduna, da kuma sukar irin rawar da wasu kasashen yankin Gulf ke takawa dangane da goyon bayan Isra’ila ne ya jawo aka kakaba masa takunkumi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *