Jihar Legas, a Najeriya, za ta karɓi baƙuncin bikin bayar da kyaututtuka na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) na 2026 a ranar Litinin, 7 ga watan Disambar wannan shekara.
A na sa ran masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afirka za su taru don murnar gagarumar nasara a fagen ƙwallon ƙafa ta Afirka.
Wannan babban biki zai tara wasu daga cikin manyan ‘yan wasa, koca-kocai, kungiyoyi, tawagar ƙasashe da kuma fitattun mutane a fagen ƙwallon kafa na nahiyar don sheda karrama waɗanda suka fi fice a ciki da wajen fili.
CAF ta tabbatar da Najeriya a matsayin mai masaukin baki ta 2026, inda aka zaɓi Legas a matsayin wurin da za a gudanar da babban taron.
-
Najeriya za ta kara da Spaniya, da Turkiyya da Masar a gasar…
-
Fury ya gayyaci Trump zuwa kallon karawar sa da Joshua
-
Yadda Senegal ta doke Sand Eagles a wasan sada zumunta a Kaduna
Ana sa ran bikin bayar da kyaututtukan zai janyo fitattun mutane daga fagen ƙwallon ƙafa na Afirka, ciki har da jami’an CAF, wakilan kungiyoyin kwallon kafa na kasa, ‘yan wasa, koca-kocai, shugabannin kungiyoyi da sauran muhimman masu ruwa da tsaki.
Kyaututtukar da za a bayar yayin taron sun haɗa da kyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afirka na maza da na mata, da Gwarzon Ɗan Wasa na Kungiyoyi, da Matashin Ɗan Wasan Shekara, da Kocin Shekara, da Tawagar Ƙasa ta Shekara, da Ƙungiyar da ta fi takarawa a Shekara da kuma Kwallo mafi kyau ko kayatarwa da aka ci a Shekara.