Kamfanin Mai na Dangote ya sake garzayawa gaban kotu domin kalubalantar lasisin shigo da man fetur da Hukumar NMDPRA ta bai wa ‘yan kasuwa da kuma Kamfanin Mai na Kasa.
Cikin karar da Dangote ya shigar gaban Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (Attorney-General), ya bukaci kotu ta soke lasisin shigo da mai da hukumar ta bayar.
Dangote ya bayyana cewa bayar da lasisin ya saba wa dokokin kasa, sannan ya saba wa umarnin kotu na baya da ya nemi kowa ya tsaya a matsayinsa wato (status quo).
Kamfanin ya zargi NNPC da sauran masu ruwa da tsaki da yunkurin gurgunta jarin sa na dala biliyan 20, inda ya koka kan yadda ake hana matatarsa danyen mai na gida, yayin da kuma ake komawa ga shigo da tatacce daga ketare.
A nasa bangaren, kamfanin NNPC yayi martanin cewa shima zai shigar da korafi na gaggawa domin kalubalantar hurumin shigar da wannan kara da kuma hakkin da Dangote ke da shi na yin hakan.
A cikin takardar rantsuwa da kamfanin ya gabatar, ya bayyana cewa Dangote bashi da hurumin shigar da kowacce irin kara akan NNPC.
Kamfanin ya kalubalanci albarkatun mai da matatar Dangote ke samarwa da cewa sun yi tsada, baya ga nuna son rai na saukewa da tayar da farashinsu a duk lokacin da aka ga dama.
Sannan NNPC ya zargi matatar ta Dangote da laifin yawo tsakanin kotuna, kamar yadda ta maka hukumar dake kula da albarkatun mai (NMDPRA) gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da Legas.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, Hukumar NMDPRA ta amince da lasisin shigo da sama da tan Dubu dari bakwai na man fetur duk da ikirarin da Dangote ke yi na cewa matatarsa na da ikon samar da sama da kaso 90 cikin dari na adadin man da kasar ke bukata a kullum.
