Hukumar Kula da Ilimin Almajirai da Yaran da Ba sa Zuwa Makaranta ta Ƙasa, NCAOOSCE, ta fara ƙidaya da tantance Almajirai da makarantun Tsangaya a ƙaramar hukumar Kiru ta Jihar Kano.

An fara aikin ne a matsayin wani mataki na aiwatar da shirin Almajiri Community Ownership Initiative, wanda ya haɗa da shirin Almajiri Mai Uwar Daki, da nufin bai wa al’umma damar taka muhimmiyar rawa wajen kula da jin daɗin Almajirai, kare su da kuma tallafa musu wajen samun ilimi.

A matakin farko, hukumar ta horar da masu sa-kai 30 a fadar Hakimin Kiru, inda aka zaɓi mutum biyu daga kowace unguwa cikin unguwanni 15 na ƙaramar hukumar.

Masu sa-kan sun samu horo kan yadda za su gano da kuma ƙirga makarantun Tsangaya da Almajirai, tare da wayar da kan al’umma kan kare haƙƙin yara.

Horarwar ta kuma ƙunshi fahimtar tsarin Almajiranci da karatun Tsangaya, illolin bara a kan tituna, ka’idojin tattara bayanai, kare yara daga cin zarafi, da kuma yadda za a gudanar da tsarin yarjejeniyar da masu kula da Almajirai za su sanya hannu a kai.

Bayan kammala horon, an tura masu sa-kan zuwa unguwanni 15 na Kiru domin fara tattara bayanai.

Aikin ya ƙunshi gano adadi da wuraren da makarantun Tsangaya suke, da sunayen malaman da ke kula da su, da kuma adadin Almajirai, da shekarunsu da jihohin da suka fito.

Hukumar ta ce ana kuma duba yanayin rayuwa da karatun yaran, tare da tantance adadin waɗanda ke yin bara a kan tituna.

Bayan tattara bayanan, za a shigar da su domin nazari da amfani wajen tsara matakan tallafi da sauran shirye-shiryen da suka dace da bukatun yaran.

A wani ɓangare na aikin, masu sa-kan na wayar da kan iyalai game da Household Caregiver Undertaking Form, wato takardar yarjejeniyar da masu kula da yaran da za su shiga shirin Almajiri Mai Uwar Daki za su amince da ita.

A ƙarƙashin tsarin, masu kula da yaran za su ɗauki alhakin samar musu da abinci sau uku a rana, kulawa ta yau da kullum da kuma jagoranci mai kyau, tare da taimaka musu wajen shiga da ci gaba da karatu na zamani ko na tsarin da ba na zamani ba.

Fara wannan aiki a Kiru na daga cikin muhimman matakan farko na mayar da shirin daga matakin tattaunawa da wayar da kai zuwa matakin gano Almajirai, makarantun Tsangaya da iyalan da ke shirye su shiga tsarin.

NCAOOSCE ta ce manufar tsarin ita ce samar da wata hanya da al’umma za su kasance a sahun gaba wajen kare Almajirai, tallafa musu wajen samun ilimi da inganta rayuwarsu, tare da amfani da bayanan da aka tattara wajen tsara shirye-shiryen da za a iya faɗaɗa su zuwa wasu wurare.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *