Shugaban ƙasar Mozambique, Daniel Francisco Chapo, ya yi gargaɗin cewa za a kwace makaman da mutane ke riƙe da su ba bisa ƙa’ida ba da ƙarfi bayan nan da watan Disamba, lokacin da wa’adin shirin afuwa da ‘yan sanda suka ƙaddamar zai ƙare.
Chapo ya ce ba za a yi wa mutanen da suka miƙa makamansu kafin wa’adin ƙarshe tambayoyi, hukunta su ko tsare su ba.
Da yake jawabi a wajen bikin rufe horar da jami’an runduna ta musamman, shugaban ya buƙaci ‘yan sanda su kasance masu ladabi, ƙwarewa da kuma mutunta doka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron al’umma.
- An kashe mutum uku a hare-haren da aka kai filayen jiragen saman Saudiyya
- Arteta ya sabunta kwantiraginsa da Arsenal har zuwa 2030
- Trump da Xi sun gana a Fadar White House, sun tattauna tsaro da fasahar AI
Ya ce ƙwarewa ta musamman ba ta nufin mutum ya fi ƙarfin doka. A maimakon haka, duk lokacin da runduna ta ƙara ƙarfin gudanar da ayyukanta, wajibi ne ta ƙara nuna ladabi da bin ƙa’idoji.
Ya jaddada cewa amfani da ikon da aka ba jami’an tsaro dole ne ya kasance cikin mutunta haƙƙin ɗan Adam da ‘yancin da kundin tsarin mulki ya ba ‘yan ƙasa.
Haka kuma, Chapo ya yi kira da a ci gaba da zuba jari wajen horas da jami’an ‘yan sanda, inda ya ce tsaron al’umma na da muhimmanci wajen cimma ‘yancin kai ta fuskar tattalin arziki, kiyaye zaman lafiya, kare ikon ƙasa da kuma tabbatar da tsaron iyakokin ƙasar.
Dangane da ƙara samun yawaitar laifuffuka, ciki har da safarar mutane da miyagun ƙwayoyi, garkuwa da mutane, manyan laifuffukan ƙungiyoyi da laifuffukan yanar gizo, Chapo ya buƙaci ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro domin inganta hanyoyin tunkarar waɗannan barazanar.
Lardin Cabo Delgado da ke arewacin Mozambique na fuskantar hare-haren masu tayar da ƙayar baya masu ikirarin jihadi tun shekarar 2017.
Sai dai Chapo ya ce yanayin tsaro a yankin ya inganta idan aka kwatanta da yadda yake a cikin shekaru biyu da suka gabata, sakamakon ƙoƙarin jami’an tsaron ƙasar, tare da taimakon sojojin Rwanda da Tanzania wajen yaƙi da ta’addanci.