Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT), Nyesom Wike, ya ce haɗin gwiwar siyasa ta Rainbow Coalition da ke tallafa wa sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027 ba ta da nufin raunana jam’iyyar APC, yana mai cewa gwamnonin jam’iyyar ba su da dalilin nuna fargaba.
Wike ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja ranar Talata, inda ya ce ƙungiyar ta haɗa mambobin APC da masu goyon bayan Tinubu daga wasu jam’iyyun siyasa domin cimma manufa ɗaya.
Ministan, wanda ke kula da ayyukan haɗin gwiwar a Jihar Rivers da Abuja, ya jaddada cewa APC ce za ta kasance jam’iyyar da Tinubu zai yi takara a ƙarƙashinta, yayin da masu goyon bayansa daga sauran jam’iyyu za su iya taimakawa wajen cimma wannan buri.
- Sojoji sun kama mutum huɗu da ake zargi da safarar makamai a Filato
- Pantami ya ba INEC wa’adin kwanaki uku ta saka sunansa cikin jerin ’yan takarar gwamnan Gombe
Ya yi watsi da zargin cewa haɗin gwiwar za ta haifar da rarrabuwar kawuna a APC ko kuma ta sa mambobinta sauya sheƙa, yana mai cewa babu wata matsala da ya sani dangane da tsarin.
Wike ya ce yanayin siyasa ya bambanta daga jiha zuwa jiha, don haka ya dace a yi la’akari da muradun yankuna yayin da ake neman haɗa kan masu goyon bayan shugaban ƙasa.
Ya ƙara da cewa irin wannan haɗin gwiwa ba sabon abu ba ne a siyasar Najeriya.
Ministan ya bayyana cewa manufar ƙungiyar ita ce tallafa wa sake zaɓen Tinubu da kuma ci gaba da abin da ya bayyana a matsayin nasarorin gwamnatinsa.
Ya buƙaci ’yan Najeriya su tantance ayyukan shugaban ƙasa bisa sakamakonsu, maimakon bambancin jam’iyya ya rinjayi ra’ayinsu.