Tawagar Flamingos

Tawagar ’Yan matan Najeriya na ’yan ƙasa da shekaru 17, wato Flamingos, za ta fara fafatawa a gasar Kofin Duniya na Mata na ’yan ƙasa da shekaru 17 na shekarar 2026 da ƙasar Poland a ranar Asabar, 17 ga Oktoba, 2026.

Najeriya na fatan haskakawa a gasar fiye da yadda ta yi a gasar da ta gabata, yayin da aka fitar da ita a matakin zagaye na 16 bayan da ƙasar Italiya ta doke ta da ci 4-0.

Tawagar Flamingos ta yi gwagwarmaya sosai a lokacin neman gurbin shiga gasar, inda ta doke Guinea da Jamhuriyar Benin domin samun gurbin wakiltar Najeriya a Marokko.

A nata ɓangaren, ƙasar Poland ta dawo gasar ne bayan ta kasa halartar gasar a shekarar 2025.

Haduwarsu ta ƙarshe ita ce a shekarar 2024 a ƙasar Dominican Republic, inda suka kai matakin kwata fainal kafin daga bisani wadda ta lashe gasar, wato Korea DPR, ta doke su.

Wannan shi ne karo na farko da Najeriya da Poland za su haɗu a wannan mataki, inda tawagar ta Flamingos ke burin fara gasar da nasara.

Najeriya tana rukunin B ne tare da Poland, da Puerto Rico, da kuma mai riƙe da kofin, wato ƙasar Korea DPR.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *