Kwankwaso, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na facebook, ya nuna damuwa kan abin da ya kira hare-haren yaƙin neman zaɓe da jam’iyyarsa na ADC a ke kai masa, da Obi da jam’iyyarsu ta Nigeria Democratic Congress (NDC).
Ya ce irin waɗannan hare-hare ba su da amfani, maimakon jam’iyyar ta mayar da hankali wajen bayyana cancanta da manufofin ɗan takararta.
- IGP Disu ya jaddada muhimmancin amfani da bayanan sirri wajen yaƙi da ta’addanci
- Hukumar shige da fice ta Gambia ta cafke mutane 35 da ake zargin shirin yin ƙaura ba bisa ƙa’ida ba
- An cire Najeriya daga Gasar WAFU B ta U17, kuma ta rasa tikitin Zuwa AFCON da Gasar kofin duniya
Ya zargi kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC da ƙoƙarin yaɗa zargin cewa da shi Obi na iya janye tikitinsu domin goyon bayan ɗan takarar ADC.
Kwankwaso ya jaddada cewa ba za su janye takararsu ba, yana mai cewa suna da ƙwarewa da shirye-shiryen jagorantar Najeriya.
Ya kuma bukaci ADC da ta mayar da hankali wajen mayar da martani kan zarge-zargen da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi wa ɗan takararta, maimakon kai hari kan shugabannin NDC.
Kwankwaso ya ce tikitin takararsa da Obi ba ya aiki a madadin APC ko wani ɗan takararta, ya kuma bayyana cewa, a ra’ayinsa, gwamnatin APC ta gaza wajen biyan buƙatun ’yan Najeriya, yayin da ADC ba ta bayar da wata mafita mafi kyau ba.
Ya ce tikitin NDC na da burin haɗa kan ’yan Najeriya da kuma magance matsalolin tsaro, ilimi, noma, ababen more rayuwa, kiwon lafiya da tattalin arziki.
Ya yi kira ga magoya bayansa da sauran ’yan Najeriya da su ci gaba da mara wa jam’iyyar baya domin samun nasara.