Tawagar Nasarawa United

An bai wa ‘yan wasan ƙungiyar Nasarawa United kyautar Naira miliyan 1 sakamakon nasarar da suka samu da ci 2-0 a kan Inter Lagos a ranar Lahadi a filin wasa na Mobolaji Johnson Arena da ke Onikan, a JiharLagos.

Wannan ita ce nasara ta farko da ƙungiyar ta Solid Miners ta samu a waje a kakar wasan 2026/27 ta Gasar Firimiyar Najeriya, wato NPFL.

Haka kuma, nasarar ta kasance mafi girman adadin kwallaye da Nasarawa United ta zura a waje a tarihin gasar NPFL.

Kelechi Ogbodo ne ya fara zura kwallo a ragar a minti na 11 kafin Ugochukwu Leonard ya kara ta biyu ga bakin a bayan minti biyar.

Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Nasarawa, Jibril Abdullahi Ibrahim, da Babban Sakatare, Stephen Iliya Sasetu ne suka raba kudin ga tawagar domin nuna jin dadinsu kan kokarin da ‘yan wasan suka yi.

Tawagar Mbwas Mangut din ta koma matsayi na biyar a teburin gasar ta NPFL inda take da maki 14 daga wasanni tara.

Nasarawa United za ta karbi bakuncin Enyimba wacce ta lashe kofin sau tara a filin wasa na Lafia domin buga wasan mako na 10 a ranar Lahadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *