Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya ce bai ce ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje su daina tallafa wa iyalansu, sai dai yana son a gina ƙasar da jama’a ba za su dogara da ’yan uwansu wajen biyan buƙatun yau da kullum ba.

Obi ya bayyana hakan ne a martaninsa kan abin da ya kira karkatar da saƙonsa da abokan hamayyarsa na siyasa suka yi, duk da cewa ofishinsa na yaɗa labarai ya riga ya fitar da sanarwar ƙarin bayani.

Ya yaba wa ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje bisa sadaukarwar da suke yi wajen taimaka wa iyalansu, ciki har da biyan kuɗin makaranta, magani, haya da abinci, yana mai cewa gudummawarsu ta cancanci girmamawa.

Ya ce manufarsa ita ce a gina Najeriya mai samar da ayyukan yi, ingantaccen ilimi, sauƙaƙa samun kiwon lafiya da damammakin tattalin arziki ga ’yan ƙasa.

Obi ya jaddada cewa ba ya son ’yan Najeriya a ƙasashen waje su yi watsi da iyalansu, sai dai yana fafutukar ganin Najeriya ba ta yi watsi da al’ummarta ba, inda ya yi addu’ar Allah ya albarkaci ’yan Najeriya a gida da ƙasashen waje da kuma ƙasar baki ɗaya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *