Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa filin wasa na Ranchers Bees da ke Kaduna, inda ake gudanar da bikin ƙaddamar da kamfen ɗin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Dubban magoya bayan jam’iyyar APC ne suka hallara a filin wasan domin halartar taron, yayin da manyan jiga-jigan jam’iyyar da jami’an gwamnati suka taru domin bikin ƙaddamar da kamfen ɗin.

Tun kafin isowar shugaban ƙasar, ministoci da gwamnonin jihohi da dama sun riga sun isa wajen taron, inda suke jiran isowarsa.

Isowar Tinubu ta zo ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke shirin fara wani muhimmin mataki na yaƙin neman zaɓenta gabanin babban zaɓen 2027.

Taron yana gudana ne a Kaduna, inda magoya bayan jam’iyyar suka taru domin nuna goyon bayansu ga jam’iyyar APC da kuma shirye-shiryenta na zaɓe mai zuwa.