Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya ce gwamnatinsa za ta mayar da bunƙasa noma, masana’antu, ilimi da kiwon lafiya cikin manyan manufofinta idan ya lashe zaɓen 2027.
Obi ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar bayan ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a Abuja ranar 26 ga Oktoba, 2026, inda ya ce zai yi aiki domin rage tsadar rayuwa da fitar da ’yan Najeriya daga talauci.
Ya ce bayan dawo da tsaro, gwamnatinsa za ta taimaka wa manoma su koma gonakinsu, ta samar da masana’antun sarrafa amfanin gona kusa da wuraren noma, tare da tallafa wa jihohi da yankuna wajen bunƙasa kayayyakin da suka fi dacewa su samar.
- Matawalle ya ce baje kolin AFRIDEX 2026 zai bunƙasa kera kayan tsaro a Najeriya
- FRSC ta aika allunan lambobin rajistar motoci 19,560 zuwa Abuja cikin Oktoba
Obi ya kuma yi alƙawarin bunƙasa Arewa ta hanyar mayar da ita cibiyar noma da masana’antun sarrafa amfanin gona, yana mai cewa hakan zai ƙara ƙarfin masana’antu da bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya.
A fannin ilimi da kiwon lafiya, ya ce gwamnatinsa za ta yi aiki da gwamnatocin jihohi wajen inganta makarantu, horar da malamai da inganta albashinsu, tare da bayar da tallafi domin rage nauyin kuɗin karatu.
Ya kuma yi alƙawarin samar da tallafi ga muhimman fannoni kamar noma da makamashi domin rage tsadar rayuwa da inganta rayuwar jama’a.