Fasahar sadarwa, likitanci, jiragen sama, injiniyanci da harkokin kuɗi na daga cikin fannoni biyar da suka fi biyan albashi mai tsoka a Afirka a shekarar 2026, yayin buƙatar ƙwararrun ma’aikata ke haɓaka albashin da ake biya a sassan nahiyar.
Rahoton ya nuna cewa injiniyoyin manhajoji da masu haɓaka shirye-shiryen kwamfuta na samun tsakanin dala 27,311 zuwa dala 58,642 a shekara, musamman a ƙasashe kamar Najeriya, Kenya da Afirka ta Kudu.
- Babban hafsan sojin Najeriya ya yaba wa dakarun Birged ta 4 kan ƙwarewarsu a Edo
- Gwamnan Neja ya yi alƙawarin ci gaba da tallafa wa taron Kiristoci na SHOUT
Waɗanda suka ƙware a fannonin fasahar AI, koyon na’ura da fasahar Blockchain na cikin waɗanda ake buƙata sosai.

Masana lissafin haɗari da hasashen kuɗi, waɗanda aka fi sani da Actuaries, na samun tsakanin dala 50,000 zuwa dala 90,000 a shekara. Ana matuƙar buƙatar ƙwararrun a wannan fanni a ƙasashen Afirka ta Kudu, Kenya da Mauritius.
Haka kuma, manajojin fasahar sadarwa da manyan injiniyoyin manhajoji na samun tsakanin dala 40,000 zuwa dala 100,000 a shekara, gwargwadon ƙwarewa da nauyin aikin da suke yi.

A ɓangaren sufurin jiragen sama kuwa, matuƙan jiragen sama da ke gudanar da zirga-zirgar ƙasa da ƙasa na samun tsakanin dala 60,000 zuwa dala 90,000 a shekara.

Injiniyoyin haƙar ma’adinai sun kasance a matsayi na biyar a jerin, inda suke samun tsakanin dala 60,000 zuwa dala 100,000 a shekara, musamman a Afirka ta Kudu, Botswana da Zambiya.

Rahoton ya danganta yawan albashin da ake biya a waɗannan fannoni da ƙwarewa, shugabanci da kuma buƙatar ƙwararrun ma’aikata.
Rahoton ya ƙara da cewa, yayin da tattalin arzikin ƙasashen Afirka ke bunƙasa da samun sauye-sauyen zamani, buƙatar ƙwararrun ma’aikata a fannonin fasaha, likitanci, injiniyanci, kuɗi da sufurin jiragen sama na iya ƙaruwa.