Babban hafsan sojin Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya yaba wa dakarun Birged ta 4 bisa ladabi, ƙwarewa da kuma yadda suke gudanar da ayyukansu na tabbatar da tsaro a Jihar Edo.
Shaibu ya bayyana hakan ne yayin ziyarar aiki ta farko da ya kai hedikwatar Birged ta 4 da ke Benin City ranar Juma’a, 6 ga Nuwamba, 2026, inda ya tabbatar wa sojojin cewa rundunar za ta gyara musu gidajen zama domin samar musu da yanayin rayuwa mai kyau.
Ya kuma yi alƙawarin samar da sabuwar motar bas domin magance matsalolin sufuri a rundunar, tare da tabbatar da cewa jami’an soji da iyalansu, ciki har da ’ya’yansu, za su samu ingantattun cibiyoyin kula da lafiya.
- Tinubu ya taya Flamingos murnar kai wa wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya
- Kwamishinonin APC sun amince da manufofin yaɗa saƙonnin gwamnati gabanin zaɓen 2027
Shaibu ya ce jin daɗin dakarun na daga cikin muhimman abubuwan da ke taimaka wa rundunar wajen gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Babban hafsan ya buƙaci sojojin su ci gaba da nuna ladabi, ƙwarewa da biyayya, tare da gudanar da ayyukansu bisa doka, mutunta haƙƙin fararen hula da kare rayukan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
Ya kuma umarce su da su ɗauki matakan da suka dace kan masu aikata laifuka a yankunan da ke ƙarƙashin kulawarsu.
Tun da farko, kwamandan Birged ta 4, Birgediya Janar Ahmed Balogun, ya yi wa babban hafsan bayani kan halin tsaro a yankin da rundunar ke kula da shi, da kuma ƙalubalen gudanarwa da kayan aiki da suke fuskanta.

Ya gode masa bisa ziyarar da alƙawuran inganta walwalar sojoji, tare da tabbatar da cewa dakarun za su ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da nasarorin da aka samu a fannin tsaro.
Ziyarar ta ƙunshi sanya hannu a kundin baƙi, bayar da kyaututtukan tunawa, dasa bishiya da ɗaukar hotuna.

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya ta Birged ta 4, Kyaftin Kennedy Anyanwu, ya fitar.