Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da tallafa wa taron Kiristoci na shekara-shekara mai suna SHOUT, wanda aka gudanar a karo na takwas a Cibiyar Baje Kolin Kasuwanci da ke Minna.

Bago ya bayyana hakan ne yayin halartar taron, inda ya ce kowane mutum na da ’yancin yin addininsa, yana mai cewa Allah ya halicci mutane ne domin su zauna lafiya tare da taimaka wa juna wajen samun ci gaba.

Gwamnan ya bayyana cewa wannan lokaci ne na farin ciki da murna, yana mai jaddada muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al’ummar jihar ba tare da la’akari da bambancin addini ba.

Tun da farko, mai shirya taron, Fasto PeteRock Sadiq, ya gode wa gwamnan bisa halartar taron a duk shekara tun bayan hawansa mulki, yana mai cewa yadda yake ba taron muhimmanci abin ƙarfafa gwiwa ne ga Kiristoci.

Gwamnan ya halarci taron tare da mataimakinsa, Yakubu Garba, mambobin majalisar zartarwa ta jihar da sauran manyan jami’an gwamnati, kamar yadda mai magana da yawun gwamnan, Bologi Ibrahim, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar ranar 6 ga Nuwamba, 2026.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *