Najeriya ce kan gaba cikin ƙasashen Afirka 12 da suka fi ƙarancin wakilcin mata a majalisun dokokinsu a shekarar 2026, inda mata ke da kashi 4.2 cikin 100 na kujerun majalisar dokokin ƙasar, kamar yadda wani rahoto ya nuna.

Aljeriya ce ke biye da Najeriya da kashi 6.1, sai Gambiya mai kashi 8.6, Botswana mai kashi 9, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mai kashi 9.4 da Laberiya mai kashi 11 cikin 100.

Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ce ke matsayi na bakwai da kashi 12.8, yayin da Ghana take matsayi na takwas da kashi 14.5.

Rahoton ya ce daga cikin mambobin majalisar dokokin Ghana 276, mata 40 ne, bisa bayanan Ƙungiyar Majalisun Dokoki ta Duniya (IPU).

Jamhuriyar Kongo da São Tomé da Príncipe suna matsayi na tara a tare da kashi 14.6 kowannensu, sai Côte d’Ivoire mai kashi 14.9, yayin da Tunisiya ke da kashi 15.8, wanda shi ne mafi girma a cikin ƙasashen 12 da aka lissafa.

Rahoton ya nuna cewa duk ƙasashen da ke cikin jerin suna da wakilcin mata ƙasa da kashi 16 cikin 100 a majalisunsu.

Ya kuma bayyana cewa Ghana ta kafa dokar daidaiton jinsi ta shekarar 2024 domin inganta wakilcin mata da shigarsu cikin harkokin yanke shawara, duk da cewa har yanzu adadinsu a majalisa bai kai kashi 15 cikin 100 ba.

Bayanan sun nuna yadda mata ke da ƙarancin wakilci a majalisun dokoki a waɗannan ƙasashe, amma rahoton ya jaddada cewa ƙididdigar ba ta auna yawan shigar mata cikin zaɓe, jam’iyyun siyasa ko sauran fannoni na rayuwar al’umma ba.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *