Ma’aikatar Jinƙai da Rage Talauci ta Tarayya ta bayyana cewa babu buƙatar yin rajista ko neman tallafi kafin mutum ya amfana da shirin bayar da tallafin gaggawa da daidaita rayuwar al’umma na ƙasa (NERSI).
Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta ma’aikatar, Janet McDickson Noah, ce ta bayyana hakan a cikin sanarwar da ta fitar domin ƙarin haske kan shirin da aka ƙaddamar don tallafa wa gidaje masu ƙaramin ƙarfi sakamakon tsadar rayuwa.
Ta ce za a zaɓi waɗanda za su amfana ne daga rajistar gidaje masu ƙaramin ƙarfi ta ƙasa da bayanan tantance katin shaida na ƙasa, bisa la’akari da matakin talauci da buƙatar tallafi.
- Najeriya da Turkiyya za su ƙarfafa haɗin gwiwar kafafen yaɗa labarai da yaƙi da yaɗa labaran ƙarya
- Najeriya ce ƙasa mafi ƙarancin wakilcin mata a majalisa a Afirka
Ma’aikatar ta jaddada cewa babu wani mutum ko wakili da zai iya yin katsalandan wajen zaɓen waɗanda za su amfana, tare da tabbatar da cewa kowane wanda aka zaɓa zai samu Naira 50,000 a matsayin tallafi, ba bashi ba, don haka ba zai buƙaci mayar da kuɗin ba.
Sanarwar ta ce za a sanar da waɗanda suka cancanta ta saƙon waya daga ɗaya daga cikin kamfanonin hada-hadar kuɗi ta zamani da aka amince da su.
Ta kuma gargaɗi jama’a da kada su bai wa kowa lambobin sirrin katin banki (PIN), kalmar sirri ta amfani sau ɗaya (OTP) ko lambar tantance asusun banki (BVN).
Ma’aikatar ta buƙaci duk masu tambaya ko ƙorafi kan shirin da su tuntubi layin NERSI mai lamba 0700-022-2222, tana mai cewa za ta tabbatar da gudanar da shirin cikin gaskiya, riƙon amana da mutunta waɗanda za su amfana, bisa tsarin Renewed Hope na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.