Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya buƙaci al’ummar Musawa da su sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027, domin rama irin damar da ya ce shugaban ya samar wa yankin.

Radda ya yi wannan kira ne a wajen gangamin kamfen ɗin Tinubu-Dikko na 2027 a Musawa, inda ya yi nuni da muƙaman gwamnatin tarayya da aka bai wa ’yan yankin, musamman Ministar Fasaha, Al’adu da Yawon Buɗe Ido, Hannatu Musa Musawa.

Gwamnan ya bayyana naɗe-naɗen a matsayin alamar amincewar Tinubu da al’ummar yankin, inda ya kuma ambaci Muntaqa Jikamshi da wasu da suka amfana da damar.

Dangane da ayyukan more rayuwa, Radda ya tabbatar wa mazauna yankin cewa za a fara aikin samar da ruwan sha na Musawa da kuma gyaran madatsar ruwa da ta lalace a mako mai zuwa.

A yayin gangamin, an raba babura 200, yayin da mata 1,050 da ɗalibai sama da 800 daga ƙananan hukumomin Musawa da Matazu suka samu tallafin Naira 50,000 kowannensu.

Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Musawa da Matazu, Abdullahi Aliyu Ahmed, wanda aka fi sani da Dujiman Katsina, ne ya jagoranci shirin bayar da tallafin.

Dujiman Katsina ya kuma yi alƙawarin ƙarin babura 1,000 ga al’ummomin ƙananan hukumomin biyu, tare da shirin raba kayan tallafi ga mutanen da rikicin tsaro ya raba da muhallansu a Matazu.

Daraktan Janar na kwamitin kamfen ɗin Tinubu-Dikko na 2027, Ahmed Musa Dangiwa, ya yaba wa jama’a bisa halartar gangamin, yayin da shugaban APC na jihar, Bishir Gambo Saulawa, ya buƙaci a ci gaba da haɗin kan jam’iyya, sannan Ministar Hannatu Musa Musawa ta yi kira da a kiyaye zaman lafiya da haɗin kai.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *