An gudanar da shirin ne tare da haɗin gwiwar cibiyar ba da shawarwari kan dokokin binciken laifuka ta hanyar fasahar zamani (FEDLAC), inda aka kammala horaswar a ranar Asabar, 7 ga Nuwamba, 2026, a makarantar horas da jami’an EFCC da ke Karu, Abuja.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, wanda mataimakin shugaban makarantar horas da jami’an hukumar, Joseph Ogwiji, ya wakilta, ya ce ingantaccen bincike shi ne ginshiƙin nasarar gurfanar da masu laifi a kotu.
- ’Yan sanda sun kubutar da mutum biyu da aka yi garkuwa da su a Yabo
- Wike ya yi alƙawarin ba kansilan da duk ya lashe mazaɓarsa Naira miliyan 10
Olukoyede ya jaddada muhimmancin gano shaidu, tattara su, tantancewa, adana su da gabatar da su bisa ƙa’idojin doka, yana mai cewa duk wani kuskure a waɗannan matakai, ciki har da na shaidu, na iya kawo cikas ga nasarar shari’a.
Babban jami’in FEDLAC kuma jagoran horaswar, Farfesa Alaba Omolaye-Ajileye, ya ce shirin zai taimaka wajen inganta yadda jami’an EFCC ke gina hujjojin shari’a, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin masu gudanar da bincike da masu gabatar da ƙara.
Horon, wanda aka gudanar cikin rukuni biyu na tsawon kwanaki uku kowanne, ya ƙunshi darussa kan binciken kimiyya, tantance takardu, sarrafa bayanan sirri, da kuma dabarun gabatar da ƙara kan laifukan kuɗi.