Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF) ta sauya ranar gudanar da bikin bayar da kyaututtukanta na shekarar 2026, daga 7 ga Disamba zuwa 2 ga Disamba.
Bikin, wanda za a gudanar a gidan wasan kwaikwayo na ƙasa (National Theatre) da ke Legas, Najeriya, zai haɗa fitattun ’yan wasa da sauran masu ruwa da tsaki a ƙwallon ƙafa ta Afirka.
- Wike ya ce Naira miliyan 10 ga kansiloli lada ne, ba na sayen ƙuri’u ba
- Majalisar Wakilai ta ɗage komawa zaman majalisa zuwa Laraba
CAF ta sanar da sabon jadawalin ne a ranar 11 ga Nuwamba, 2026, inda ta tabbatar da cewa bikin zai gudana a ranar 2 ga Disamba, 2026.
Tun da farko, CAF ta tsara gudanar da bikin ne a ranar 7 ga Disamba, 2026, kafin daga bisani ta sauya shi zuwa 2 ga Disamba, ba tare da bayyana dalilin sauyin ba.