Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya (NCoS) ta tabbatar da tserewar fursunoni biyu daga gidan gyaran hali da ke Okene, Jihar Kogi.
Kakakin hukumar, Jane Osuji, ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ta ce fursunonin sun tsere ne a ranar Lahadi, 8 ga Nuwamba, 2026.
Hukumar ta ce tun bayan faruwar lamarin ta fara ƙoƙarin sake kama fursunonin tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro.
- Sojoji sun kashe ’yan ta’adda biyu, sun kuɓutar da mutane uku a Adamawa
- Wike ya ce Naira miliyan 10 ga kansiloli lada ne, ba na sayen ƙuri’u ba
Ta kuma bayyana cewa babban kwanturolan hukumar ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano yadda fursunonin suka samu damar tserewa da kuma duk wani sakaci da ka iya haddasa lamarin.
Hukumar ta tabbatar wa jama’a cewa tana ɗaukar matakan da suka dace domin sake cafke fursunonin, tare da alƙawarin fitar da ƙarin bayani idan an samu sahihan bayanai.