Cibiyar yaƙi da yaɗuwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce ba a samu sabon wanda ya kamu da cutar Ebola ba, kwanaki 21 bayan tabbatar da shigar da cutar nau’in Bundibugyo daga ƙasar Uganda zuwa Najeriya.

Sai dai Darakta-Janar na hukumar, Dakta Jide Idris, ya yi gargaɗin cewa Najeriya na fuskantar barazanar wasu cututtuka masu yaɗuwa da suka haɗa da Dengue, Chikungunya, Diphtheria, cutar sankarau da kuma zazzabin Lassa.

Ya ce hukumar na ci gaba da sa ido sosai da gudanar da bincike kan waɗanda ake zargin sun kamu da cututtuka, domin tabbatar da cewa ba a samu sake yaɗuwar Ebola ko wasu cututtuka ba.

NCDC ta tabbatar da samun cutar Dengue a jihohin Sakkwato da Zamfara, yayin da aka kuma samu cutar Chikungunya a Jihar Sakkwato. Hukumar ta tura ƙungiyoyin gaggawa domin taimaka wa jihohin da abin ya shafa.

Hukumar ta kuma ce tana ƙarfafa shirye-shiryen yaƙi da cutar sankarau da kuma zazzabin Lassa da ake sa ran samun ƙaruwar kamuwarsa a wannan lokaci, tare da ci gaba da ƙoƙarin dakile cutar Diphtheria.

NCDC ta shawarci ’yan Najeriya da su kula da tsafta, kare kansu daga sauro da beraye, tabbatar da yi wa yara cikakken allurar rigakafi tare da zuwa asibiti da zarar sun fara rashin lafiya.

Ta jaddada cewa ba duk zazzabi ne na zazzaɓin cizon sauro ba.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *