Rundunar ’yan sandan Najeriya ta ce ta kuɓutar da fasinjoji 10 da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a ranar 3 ga Nuwamba a Orita Fufu, Awa Ijebu, Jihar Ogun.

Sanarwar ta ce an kuɓutar da fasinjojin motar bas ɗin kamfanin New Edo Line ne a ranar 7 ga Nuwamba, ba tare da sun samu rauni ba. Daga bisani, jami’an yaƙi da garkuwa da mutane sun kai samame maboyar waɗanda ake zargi a kan hanyar Ibadan zuwa Ijebu Ode.

A yayin musayar wuta, rundunar ta ce an kashe ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi, yayin da wasu huɗu suka tsere da raunukan harbin bindiga. An ƙwato bindigar AK-47 guda ɗaya, alburusai 20, kuɗi Naira 1,376,800 da wayar hannu.

A wani samame mai kama da wannan rundunar ’yan sandan Najeriya ta ce jami’an tsaro sun ceto mutane biyar da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a ƙauyen Utange, gundumar Tor-Donga ta Ƙaramar Hukumar Katsina-Ala, Jihar Benuwe.

Sanarwar ta ce ’yan bindigar da ake zargin masu biyayya ne ga wani shugaban ’yan bindiga mai suna Konyo sun kai hari ƙauyen a ranar 8 ga Nuwamba. Jami’an ’yan sanda, rundunar PMF da Operation Whirl Stroke sun bazama daji domin kuɓutar da mutanen.

Sai dai rundunar ta ce uku daga cikin waɗanda aka sace sun samu munanan raunuka, kuma sun rasu a kan hanyarsu ta zuwa asibiti, yayin da aka kuɓutar da sauran biyun ba tare da rauni ba.

Ta ƙara da cewa an tura ƙarin jami’an tsaro domin kamo waɗanda suka tsere da kuma lalata sansanoninsu.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *