Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta horas da jami’anta 500 a wani shirin kwanaki uku domin inganta ƙwarewa, ladabi da bin ƙa’idojin aikin ɗan sanda.

An gudanar da horon ne daga 9 zuwa 11 ga Nuwamba, 2026, a cibiyar taron manyan jami’an ’yan sanda da ke Owerri, tare da halartar jami’ai daga sassan rundunar daban-daban, ciki har da sassan yaƙi da laifuffuka da kula da zirga-zirgar ababen hawa.

Horon ya mayar da hankali kan yadda ake gudanar da binciken ababen hawa da mutane, sintiri, kula da zirga-zirga da sauran ayyukan tsaro.

Jami’an da suka jagoranci horon sun haɗa da ACP Linus Nwaiwu da ACP Abdullahi Wase.

Da yake jawabi a madadin kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Audu Garba Bosso, mataimakinsa, DCP Hammanjoda Barka, ya buƙaci jami’an su yi amfani da ilimin da suka samu wajen inganta ayyukansu, tare da kiyaye dokoki da haƙƙin bil’adama.

Ya gargaɗe su kan karɓar rashawa, cin hanci, tsoratar da jama’a, tsare mutum ba bisa ƙa’ida ba da kuma cin zarafin ikon da doka ta ba su.

Ya kuma jaddada cewa wajibi ne jami’ai su riƙa mu’amala da jama’a cikin mutunci da girmamawa yayin gudanar da bincike da sintiri.

Game da amfani da bindigogi, DCP Barka ya tunatar da jami’an cewa dole ne amfani da ƙarfi ya kasance bisa doka, larura da daidaito, tare da ɗaukar alhakin duk wani mataki.

Ya kuma ce rundunar ba za ta lamunci rashin da’a ba, kuma za ta hukunta duk jami’in da aka samu da laifi.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *