Kwamishinan ’yan sandan Jihar Imo, CP Audu Garba Bosso, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan harbin wani mutum mai suna Gift Okoro, mai shekaru 34, a Owerri.
Sanarwar rundunar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 11 ga Nuwamba, 2026, inda wasu mutanen da ba a san ko su waye ba suka harbe Okoro. Rundunar ta ce jami’anta sun gaggauta kai ɗauki bayan samun rahoton faruwar lamarin.
- ’Yan sanda sun ceto fasinjoji 10 da aka yi garkuwa da su a Ogun
- Shugaban NYSC ya yaba wa rundunar sojoji ta 9 Brigade kan tallafin da take bai wa shirin a Legas
Kwamishinan ya umurci jami’an bincike da su gano yadda abin ya faru tare da kamo waɗanda suka aikata shi domin gurfanar da su a gaban kotu bisa tanadin doka.
Ya jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci ayyukan ƙungiyoyin asiri, rikicin ƙungiyoyin daba ko wani nau’in aikata laifi a jihar ba.
Kwamishinan ya kuma tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyinsu, tare da kira ga jama’a da su taimaka mata da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gudanar da binciken.