Jam’iyyar ADC ta yi Allah-wadai da duk wani yunƙuri na tsoratarwa ko hana ’yan Najeriya amfani da ’yancinsu na faɗin albarkacin baki, tana mai cewa jama’a na da ’yancin bayyana rashin gamsuwarsu da shugabanci.
Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar, Kola Ologbondiyan, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Sanarwar ta ce taken “BAMAYI” da ake yaɗawa na nuna ɓacin rai da rashin gamsuwar wasu ’yan ƙasa, waɗanda ke ganin an yaudare su da alkawuran jam’iyyar APC da gwamnatinta. ADC ta ce bai kamata a yi amfani da barazana, farfaganda ko tsoratarwa wajen hana jama’a bayyana ra’ayoyinsu ba.
- 2027: Rikicin siyasa na ƙara ɗaukar zafi, ‘yan Najeriya na fargabar abin da ke tafe
-
ADC ta bukaci ’yan Najeriya su yi koyi da Amurkawa kan tsadar rayuwa a zaɓen 2027
Jam’iyyar ta kuma zargi gwamnatin APC da ƙoƙarin amfani da farfaganda da dabarun hulɗa da jama’a wajen ɓoye matsalolin da ƙasar ke fuskanta, tana mai cewa babu wani kamfen na hulɗa da ƙasashen waje da zai iya sauya halin da ’yan Najeriya ke ciki.
ADC ta bayyana cewa za ta ci gaba da bin tafarkin lumana, tare da mai da hankali kan samar wa ’yan Najeriya wata sahihiyar gwamnati.
Ta kuma jaddada cewa ba za ta bari a tsorata ta ko a hana ta bayyana matsayinta ba.
Jam’iyyar ta ce tana ganin ƙaruwar rashin gamsuwar jama’a na iya shafar makomar siyasar APC, amma ba ta bayyana wata hujja mai zaman kanta da za ta tabbatar da wannan hasashe ba.