Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana hakan yayin wata ziyara da Sarah Elizabeth Crawford, mai kula da Cibiyar Haɗin Gwiwar Tsaron Iyakoki (IBSN), ta jagoranta zuwa ma’aikatar a Abuja.
Ministan ya bayyana shirin IBSN a matsayin wani muhimmin yunƙuri da ya dace da ƙoƙarin Najeriya na inganta kula da iyakoki da magance sabbin ƙalubalen tsaro. Ya tabbatar da cewa ma’aikatar za ta ba shirin goyon baya tare da yin aiki da cibiyar domin cimma manufofinsa.
- Guinea ta dakatar da shirye-shiryen gidan talabijin na RTB na Burkina Faso
- FAAC ta raba Naira tiriliyan 2.44 ga gwamnatocin Najeriya
Tunji-Ojo ya ce Najeriya na gudanar da bincike na haɗin gwiwa domin gano ainihin buƙatun ƙasar wajen tsaron iyakoki, musamman ta fuskar horar da jami’ai, samar da kayan aiki da ƙarfafa hukumomin da ke kula da iyakoki.
Ya kuma bayyana cewa Najeriya na tsara dabarun tsaron iyakoki na ƙasa tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Ƙasa da Ƙasa ta Kula da Hijira (IOM), domin samar da tsarin shekaru biyar na inganta tsaron iyakoki.
A nata jawabin, Sarah Crawford ta ce IBSN na aiki a ƙasashe tara na Yammacin Afirka, tare da tallafin ƙasashe da ƙungiyoyi shida na ƙasashen waje, ciki har da Jamus, Italiya, Amurka, Kanada, Birtaniya da Netherlands, da kuma hukumomi irin su INTERPOL.
Ta ce shirin na da nufin ƙarfafa tsaron iyakoki ta hanyar haɗin gwiwa, ingantaccen amfani da albarkatu da kauce wa maimaita ayyukan da wasu shirye-shirye ke gudanarwa.
Crawford ta ƙara da cewa binciken da ake gudanarwa a Najeriya zai taimaka wajen gano buƙatun ƙasar da kuma tsara hanyar aiki ta shekaru uku ga yankin. Ta kuma yi gargaɗi kan sabon salon shigo da sinadarai da ake amfani da su wajen samar da miyagun ƙwayoyi a cikin gida, tana mai buƙatar ƙarin horo, musayar bayanan sirri da haɗin gwiwar ƙasashen duniya domin magance barazanar tsaro.