Rundunar ta bayyana cewa jami’anta sun halarci taron ƙarshe na tsara atisayen haɗin gwiwar rundunonin sojin saman Afirka (AAAF), gabanin gudanar da atisayen NGUVU PAMOJA 2027, wanda aka tsara gudanarwa daga 28 ga Janairu zuwa 3 ga Fabrairu, 2027, a biranen Nairobi da Kisumu na ƙasar Kenya.
Taron ya taimaka wajen kammala shirye-shiryen atisayen irinsa na farko a Afirka, wanda zai haɗa da amfani da jiragen sama wajen gudanar da ayyukan agajin jin ƙai da tunkarar ibtila’i.
- ’Yan sandan Kano sun gargaɗi direbobi kan cunkoson ababen hawa a hanyar Wudil
- Abia Warriors ta naɗa Isa Ladan Bosso a matsayin sabon kocinta kan kwantiragin shekara guda
Ana sa ran kusan jami’an soji 500 daga ƙasashe daban-daban za su shiga atisayen.
NAF ta ce shiga cikin wannan shiri na ƙarfafa ƙudurin Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, na inganta shirin ko-ta-kwana, ƙwarewar aiki da kuma bunƙasa haɗin gwiwar dabarun soja da sauran ƙasashen Afirka.
Atisayen NGUVU PAMOJA 2027 zai ba rundunonin sojin saman Afirka damar haɗa ƙarfi da ƙwarewa wajen gudanar da ayyukan agajin gaggawa, musamman lokacin bala’o’i da ke buƙatar saurin kai agaji domin ceton rayuka da rage wahalhalun da al’umma ke fuskanta.