Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce saƙon fatan alheri da haɗin gwiwar siyasa tsakanin sa da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi, na samun karɓuwa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne bayan ziyarar kwanaki huɗu da ya kai wasu sassan yankin, inda ya fara daga jihar Gombe, ya wuce Potiskum da Damaturu a jihar Yobe, kafin ya isa Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Ya ce a yayin ziyarar, sun nuna ta’aziyya da alhini ga al’ummar jihohin Yobe da Borno kan matsalolin tsaro da ke ci gaba da shafar rayuwarsu, tare da jaddada buƙatar kawo ƙarshen matsalolin.

Tsohon gwamnan na Kano ya kuma ce ya yi alƙawarin cewa za su yi aiki tuƙuru wajen farfaɗo da tattalin arzikin yankin ta hanyar ƙarfafa ƙananan hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga da harkokin tattalin arziki a ƙasar.

Kwankwaso ya kuma yaba wa Peter Obi, wanda ya bayyana a matsayin ɗan uwansa, bisa ayyukan da yake gudanarwa a jihar Anambra da sauran sassan ƙasar, yana mai cewa yana farin cikin irin ƙoƙarin da yake yi.

Kwamandan ya bayyana waɗannan bayanai ne a cikin saƙon da ya wallafa, inda ya bayyana fatansa na ganin saƙon haɗin gwiwarsu ya ci gaba da isa ga al’ummar yankin da sauran sassan Najeriya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *